Dalilai da yasa zaka yi amfani da java programming language domin backend development

DALILAI DA YASA ZAKA YI AMFANI DA JAVA AZAMAN BACKEND DEVELOPMENT

Java: shahararren programming language neh Wanda ake amfani da shi wajen kirkirar manhaja ta desktop da kuma manhaja ta wayar hannu domin sarrafa bayanai masu girman gaskiye, haka kuma domin backend development da dai sauransu.

Oracle, wato kamfanin da take da mallakin java ta ruwaito cewa yaren java yana aiki neh akan na'urori wajen billion 3 a duniya, hakan ya sanya yaren ta zama shahararre. 

 

Awannan rubutu nawa zan tattauna game da abubuwa kaman haka:

 1. Tarihin java.

 2. Dalilai da yasa ake amfani da java azaman backend development.

 3. Manyan kamfononin fasaha da su already yanzu haka suna amfani da yaren java azaman backend development.

 4. manyan frameworks na java wadanda ake amfani da su azaman backend development.

5. Abu na karshe shine zamu tattauna amfani da kuma rashin amfani(disadvantage) na amfani da yaren java domin backend development

Abu Na Farko: Tarihin Java

Yaren Java Ta fara aiki neh a shekarar 1991 alokacin da James Gosling da team nasa suka fara kirkire-kirkire da yaren java a kamfaninsa mai suna Sun Microsystems.

A shekara 1995 java ya bayyana a duniya wato kowa da kowa ya fara aiki da yaren domin aiwatar da aikace-aikace masu yawa.

Java yana daya daga cikin top three programming languages wandanda ake amfani da su a duniya domin aikin backend.

Java ya samu rank na farko a top ten programming languages a shekarar 2022.

Abu Na Biyu: Dalilai da yasa ake amfani da java azaman backend development

Abubuwan da zamu lissafo su akasa amfani da ake zamu ne domin backend development, sune kaman haka:

a. Scalability and Robustness

Java yana da type-checking(wato hanya ce da take analysing program domin ta tabbatar da value da aka yi assigning izuwa variable type da aka yi declaring sun yi daidai) mai karfi, Wanda wannan type-checking mechanism din yasa java ana amfani da shi sawon lokaci. 

Kuma java yana amfani da Java Virtual Machine(JVM) domin ta bada dynamic linking, kuma ta bada tsararren waje , sannan ta bada daman running din code na java ako ina. 

Java yana amfani da abinda ake kira memory management domin ta karawa ita java sauri wajen running code dinta, hakan nan memory management a java yana karawa web application development sauri.

b. Open Source Library

Libraries na java masu girma mafi yawansu free and open source ne (wato libraries na java code nasu kyauta ne kuma kowa yana da ikon ya gani kuma yayi aiki da su).

Amfani da libraries na java yana karawa backend din project na web programming sauri. Wato abinda ake nufi shine idan kana aikin web development yin aiki da java azaman backend din project naka zai karawa project dinka Sauri. 

Akwai libraries na java masu yawan gaskiye domin aiwatar da aiyuka kala daban-daban: irinsu logging, JSON parsing, unit testing, XML and HTML parsing, messaging, PDF and Excel reading, cryptography da sauransu.

c. Diversity

Java yaren programming ne Wanda ta dauki tsawon lokaci ana amfani da shi wanjen kirkirar manhaja ta yanar gizo(web application), manhajar wayar hannu(android application) da software tools irinsu Eclipse, IntelliJ IDEA, NetBeans IDE, da sauransu.

Yanxu yaren java ta fadada domin ana iya kirkirar manhaja ta data science, manhaja ta machine learning, manhaja ta IoT.

d. Simplicity

Wato tsari da kuma dokokin rubuta program na java yana da sauki, yana da saukin fahimta kuma tana da saukin gano error idan ta wakana acikin code.

Java bata rikitarwa kaman yadda C, C++ suke rikitarwa domin mafi yawancin features da wadannan languages din suke da shi irin su explicit pointers, storage classes, operator overloading da sauransu, duka babu an chire su a Java.

e. Security

Java tana rage security concern da hadurra ta hanya rage yawan amfani da exploit pointer. Pointer kuma value ne da yake rike memory address na wani value kuma hakan zai sa ayi amfani da unwanted memory access. Domin samun tsaro sai acire concept na pointer din gaba daya a yaren java.

f. Platform independent 

Java ita independent platform ne wato abin nufi shine ka rubuta code na java sau daya, kayi running din shi ako ina, shine da turanci "write once, run anywhere" (WORA) language.

ABU NA UKU: RASHIN AMFANIN JAVA (DISADVANTAGE)

a. Lack of Backup Facility

Java baya supporting kayan aikin backup wato bayanai da za'a yi copying dinsu don gudun rasa asalin bayanan, idan aka rasa asalin bayanan, Wanda aka yi copying dinsa idan aka yi backup sai ta dawo da bayanan amma java baya copying bayanai sannan ta dawo da su idan aka rasa original din.

b. Code Complexity

Code na java extensive ne wato abin nufi code na java yana dauke da kalmomi dayawa da dogin kalmomi, yana dauke da jimloli masu rikitarwa Wanda yake da wahalan karantawa da fahimta.

c. Speed and Performance Level

Java tana cinye space mai girma a memory haka kuma tafi native languages slow sosai irinsu C da C++, dalilin samuwar slow nashi kuwa ko wani code ana fassara shi izuwa machine-level code(wato yaren computer 0s and 1s).

ABU NA HUDU: MANYAN KAMFONONI DA SUKE AIKI DA JAVA

An ruwaito a kididdiga daga Codegym cewa kamfononi 10,130 suke aiki da yaren java. Daga kamfoni da suke aiki da java ya kunshi;

a. LinkedI

b. Uber

c. Microsoft

d. Nasa World Wind

e. Netflix

f. Airbnb

g. Google

h. eBay

i. Spotify

j. TripAdvisor

k. Intel

l. Pinterest

m. Groupon

n. Slack

o. Flipkart da sauransu

ABU NA BIYAR: MANYAN FRAMEWORKS NA JAVA DOMIN AIKIN BACKEND 

Akwai framework masu yawa na java wadanda ake amfani da su domin backend development, ko wanne tana da karfi da features, amma frameworks da zamu lissafa sune mafi shahararru;

a. Spring

b. Hibernate

c. Play

d. Strut 

Writer and Translator:

Muhammad Abdulmalik

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author