Kungiyar Dalibai Ta Kasa Reshen Jihar Zamfara (NUZAMMS) Tayi Sanadiyar Sa Wasu Dalibai Rashin Samun Damar Kammala Zangon Karshe Na Karatun Su.

Kungiyar Dalibai Ta Kasa Reshen Jihar Zamfara (NUZAMMS) Tayi Sanadiyar Sa Wasu Dalibai Rashin Samun Damar Kammala Zangon Karshe Na Karatun Su.

 

Daga: Aliyu Abdulaziz Madawaki Kucheri 

 

Abunda Ya Faru Bayan Samun Korafi Daga Mabanbantan Mutane Musamman Wadanda Muka Kammala Karatu Dasu A Kwalejin Ilimi Dake Garin Maru Ta Jihar Zamfara (Zamfara State College Of Education Maru) Cewa Akwai Akalla Kashi Sittin 60% Cikin Dari 100% Na Daliban Da Suke Zaune Gida Maimakon Ace Suna Wurin (TEACHING PRACTICE) Sakamakon Rashin Kudin Registration Da Basudq Su, Kuma Ya Kasanche Tilas ne Sai Mutum Yayi Teaching Practice Kafin Nan Ya Samu Ya Kammala Karatunsa, Wanda Kuma Anayin Teaching Practice Dinne Bayan Biyan Kudin Registration Wanda Shine Zai Bada Damar A Baka Kayayyakin Da Za'a Turaka Makaranta Domin Daukar Horan Karantarwa.

 

Bayan Samun Wannan Labarin Na Yanke Shawarar Nema Ma Wadannan Yara Taimako Daga Mutanen Mu Da Suka Saba Taimakama Diyan Talakawa Musamman A Bangaren Karatu Saboda Rashin Hali Na Iya Dauke Lalurar Karatunsu, Na Wallafa Abun A Shafina Na Facebook Akan Matsalar Da Daliban Ke Fuskanta Kasanchewar Har An Kusa Kammala Teaching Practice Din Kuma Suna Gida Zaune Basu Fara Ba Saboda Rashin Kudi.

 

Dan Lokaci Kadan Bayan Rubutun Kungiyar Daliban Ta NUZAMMS Sun Tuntube Ni Akan Matsalar Domin Ganin Sunyi Wani Abu Akai, Tareda Tabbatar Mun Cewa Babu Shakka Zasu Biyama Yaran Nan Kudin Registration Koda Mutum 50 Saboda Haka Inje In Anso Bayanan Yaran Domin Samunm A Biya masu.

 

Bayan Shaidamun Hakan Na Kara Wallafa Kamar Yanda Nayi Cewa An Samu Wadanda Zasu Taimaka Ma Yaran Nan Saboda Duk Wanda Keda Wannan Matsalar Ya Tura Bayanan Sa, (Remita) Da dai Sauransu Domin A Biya Masu, Nan Danan Wadanda Suka Samu Bayanin Suka Turo Na Hada Na Tura Masu Remitas Din Kowa, Akace Mani Anyi Zama Kuma A Bada Kudi Za'a Biya A Kirw Kowa A Bashi (Payment Receipt) Domin Yakai Shaida Makaranta A Bashi Kayan Teaching Practice Ya Cigaba.

 

Bayan Anyu Haka Ma Akwai Wani Dan Siyasa Da Ya Kirani Akan Zai Biya Masu Amma Na Fada Masa An Samu Ma Wasu Zasu Biya Yace Masha Allah. 

 

Kwana Daya Kwana Biyu A Tunani An Biya Kudi, Aka Fara Kirana Har An Kusa Gama Supervision Anji Shiru cikin Mamaki Nace Ba'a Biya Bane ? Sukace Eh . Na kira Shugabannin Kungiyar Aka Fara Cemun An Ba wani Kudi Yanzu Ko An Kira Waya Baya Dauka , Gashi Wancan Na Riga Nace Masa Anbiya Balle Na Mishi Magana.

 

Daga Karshe Dai Ko Wayata Babu Mai Dauka, Gashi Yaran Nan Sunsa Ransu Cewa Tunda Nayi Magana Akai To Kamar Anyi Angama Ne.

 

Wannan Yanzu Maganar Nan Da Nake Maku Yaran Suna Gida Zaune Wani Ma Wlh Saboda Haka Din Harya Tafi Kudu Neman Kudi Ya Yafe Karatun. 

 

Ko Ba Komi Kana Kiran Mutum Kayi Mashi Bayani Idan Akwai Wata Matsala Sai Ya Sani Domin Daukar Mataki Na Gaba.

 

Allah Yasa Mudace

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author