Wani matashi da ya Kirkiri Sabon Facebook

*ALHAMDULILLAH* 

CIGABA! CIGABA!! CIGABA!!!

 

Cikin matuqar murna da farin ciki,

Kungiyar ASOF na gabatar muku da nasarar wani hãziki, kuma jajirtaccen dalibi kuma matashi Dan Arewa daga jihar Zamfara. me suna; ABDULLAHI ABUBAKAR

 

Matashin ya samu nasarar kirkirar (Gina) software ta mu'amalar sadarwa me suna *GREENBOOK*. 

 

Greenbook kafa ce ta sada zumunta na zamani kamar Facebook, WhatsApp, Instagram, twitter da sauran su. Sai dai, features dinta sunfi kama da na Facebook da Instagram.

 

Zaka Iya posting a timeline, story, chatting, da kuma fadada kasuwancika da greenbook.

 

 *Menene alfanun amfani da greenbook akan sauran irinsu Facebook?*

 

👉  Yanada cikakken tsarin tsaro 

👉 Namu ne, na Dan Nigeria, Dan Arewa kuma matashi.

👉 Akwai tsari na katange kafar daga qazaman abubuwa (illicit content) irinsu hotunan batsa, bidiyoyin batsa, qazaman kalamai, da duk wani Abu mai cutar da hankali.

 

An gina wannan kafar bisa tsari na tsafta domin kare martaba na addini da kuma tarbiyya da al'adunmu.

 

 

Saboda haka ASOF na kira ga matasa da dalibai da su bada gudumawa wajen raya wannan kafar don cigaban Matasan Arewa da ma Nigeria baki daya.

 

Ku Danna wannan link din, domin sauke application dinsa a playstore 👇👇

 

https://play.google.com/store/apps/details?id=top.greenbook.top

 

Masu IPhone kuma zasu Iya bude profile ta wannan link din👇👇

 

www.greenbook.top

 

Wannan zaku Iya bibiyar official profile din kampanin na twitter ta👇

 

https://twitter.com/NGreenbook

 

 

🖊️imãmu Faisal Musa

 _ASOF coordinator, Kebbi state._

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author

Co founder @Blogshouse